1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kasuwancin Amirka da Turai ta ci tura

Yusuf BalaAugust 28, 2016

A cewar Tarayyar Turai Amirka na neman yi mata dole kan wasu abubuwa kan yarjejeniyar ta TTIP.

https://p.dw.com/p/1JrHW
Deutschland Hannover Messe TTIP USA
An dai dauki lokaci ana muhawara kan yarjejeniyar ta TTIP tsakanin Amirka da TuraiHoto: picture-alliance/dpa/C. Charisius

Ministan harkokin tattalin arzikin Jamus wanda kuma shi ne mataimakin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel, ya bayyana a ranar Lahadin nan cewa tattaunawa kan yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin Amirka da kasashen Turai da akewa lakabin TTIP ta gaza nasara.

A cewar Gabriel a wata tattaunawa da kafar yada labarai ta ZDF, Amirka ta fadi kasa bayan da ta ke neman yi wa kasashen na Turai karfa-karfa su kuma ba za su mika mata wuya ba sai yadda aka yi da su.

Amirka da Tarayyar Tuarai na tattaunawa kan yarjejeniyar ta TTIP tsawon shekaru uku kenan sai dai har kawowa yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba, abin da kowane bangare ke fata ya zuwa karshen wannan shekara ta 2016. Daya daga cikin abin da suke samun banbanci akansa shi ne aiyukan gona.