Yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya
May 29, 2010Ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya a duniya, sun cimma daidaito kan wani saban mataki na matsa ƙaimi da sa ido,domin mutunta wannan yarjejeniya.
Saban matakin ya ƙalubalanci Ƙasashe biyar na duniya da suka mallaki manyan makamann nukiliyar wato Amurika, Rasha,China, Fransa da Britaniya da su rage yawan wannan makamai.A ɗaya wajen, ƙasashen sun amince suyi aiki kafaɗa da kafaɗa, domin tsarkake yankin Gabas ta tsakiya daga makaman nukiliya, saboda haka,sun ƙuduri aniyar shirya taro na mussamman a shekara ta 2012 kan batun.Sannan sun yi kira da babbar murya ga ƙasashen Isra´ila, Indiya, Pakistan da Koriya ta Arewa, suma su rattaba hannu akan yarjejeniya hana yaɗuwar makaman nukiliya da suka ƙauracewa.