1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yarjejeniyar gwamnatin gambiza a Zimbabwe

Jam´iyun da ke adawa da juna a Zimbabwe sun amince da yarjejeniyar raba iko

default

Shugaba Robert Mugabe

Shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin raba madafun iko tsakanin shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da jam´iyar adawa ta MDC. A ma halin da ake ciki Mugabe da jagoran ´yan adawa Morgan Changirai sun sanya hannu kan yarjejeniyar.


A yau Juma´a al´umar Zimbabwe sun kasa kunni suna jiran ƙarin bayani na yarjejeniyar raba madafun iko da manyan jam´iyun da ba sa ga maciji da juna a ƙasar suka cimma da nufin kawo ƙarshen mummunar dambaruwar siyasa da ta addabi ƙasar bayan jerin shawarwari da suka ta´allaka kan kaf gwamnatin haɗaka.


Shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki wanda ke shiga tsakani a tattaunawar shi ya ba da sanarwar cimma yarjejeniyar a birnin Harare inda ya ke tun a farkon wannan makon a ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar wadda ta cije.


Ya ce: "An cimma yarjejeniya akan dukkan batutuwan da ke kan ajandar wannan tattaunawa. A ranar Litinin mai zuwa za´a yi bukin sanya hannun a hukumance a nan birnin Harare."


Ba a dai ba yi bayani game da abubuwan dake ƙunshe cikin yarjejeniyar ba amma Mbeki ya ce za a nuna ta ga jama´a ne bayan an yi bukin sanya mata hannu a hukumance.


Ya ce: "Dukkan shugabannin jam´iyun siyasa a Zimbabwe za su sanya hannu kan yarjejeniyar kafin a bayyana ta ga jama´a. Ko da yake dukkansu sun albarkace ta amma dukkansu su amince da a bayyana ta ga jama´a a ranar Litinin."


Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce a ranar Litinin ɗin shugabannin na Zimbabwe za su kuma gabatar da rahoto dangane da fasalin kundin tsarin mulkin ƙasar wanda zai ƙunshi sabuwar gwamnatin da aka amince kanta.


Mugabe da babban mai adawa da shi Morgan Changirai sun yi ta kai ruwa rana a tattaunawar kan raba madafun iko inda a baya bayannan jagoran na ´yan adawa ya yi kashedin cewa ba zai amince da wata yarjejeniya da za ta hana shi cikakken iko. Masharhanta sun ce batun wanda za a ba shi ikon jan akalar hukumar tsaron Zimbabwe na ɗaya daga cikin batutuwan da suka kawo ciƙas. Mugabe mai shekaru 84 wanda ya kasance gwarzo a yaƙin da ya kai ga bawa Zimbabwe ´yanci a shekarar 1980, kuma ya ke shugabancin ƙasar tun daga wannan lokaci, ya na samun cikakken goyon baya daga shugabannin hukumomin tsaron ƙasar.


A halin da ake ciki babban sakataren majalisar ɗinkin duniya Ban Ki Moon ya yaba da yarjejeniyar inda yayi fatan cewa za ta share fagen samun zaman lafiya mai ɗorewa a Zimbabwe. Ita ma Birtaniya wadda ta yiwa Zimabbwe mulkin mallaka ta ce tana sa ido ta ga irin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa.