Yarjejeniyar gina matatun mai a Najeriya | Labarai | DW | 14.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar gina matatun mai a Najeriya

Najeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar gina matatun man fetir

default

Najeriya da wani kamfanin ƙasar China sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta dala miliyan dubu 23, don gina matatun man fetir guda uku da wani wurin sarrafa man fetir. Wata sanarwar hukuma ta ce kamfanin man fetir ta ƙasa wato NNPC da kamfanin CSCEC na China suka ƙulla wannan yarjejeniya a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya. Sanarwar ta ci-gaba da cewa kamfanin NNPC zai gaggauta aikin gina matatun man a Najeriya a wani mataki na daƙile shiga da mai ƙasar da aka ƙiyasce kuɗinsa ya kai dala miliyan dubu 10. Najeriya dake zama ƙasar Afirka da ta fi samar da man fetir, ta shafe shekaru fiye da 10 tana sayen tataccen man fetir da dangoginsa daga ƙetare domin cimma buƙatu na cikin gida. Hukumomin Nijeriya dai na fatan samar da matatun, zai sa ƙasar ta sami ƙarin gangan man fetur dubu 750 a kowace rana - lamarin da kuma zai sa kamfanin man fetur na gwamnatin Nijeriya ya sami kyakkyawan matsayi a cikin jerin ƙasashen dake sayar da tataccen mai a kasuwar duniya. Hakanan sanarwar ta ce gina matatun zai kuma inganta sauye sauyen da gwamnatin Nijeriya ke yi a harkar man fetur da kuma iskar gas.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu