1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yarjejeniyar Geneva Akan Fursinonin Yaki

A shekarar 1949 aka gabatar da yarjejeniyar Geneva a game da kare lafiyar farar fula a lokacin yaki sakamakon ta'asa iri dabam-dabam da aka fuskanta a yake-yaken duniya guda biyu da suka gabata

Hoton harin da aka kai akan shelkwatar Kwamitin Red Cross na kasa da kasa a Bagadaza

Hoton harin da aka kai akan shelkwatar Kwamitin Red Cross na kasa da kasa a Bagadaza

Tun a wajejen karshen karni na 19 ne aka fara bitar matakan kare mutuncin dan-Adam a lokacin yaki. Wani abin da yayi tasirin wajen cimma yarjejeniyar Geneva game da kare hakkin fursinonin yaki a shekarar 1949 kuwa shi ne ta’asa iri dabam-dabam da aka fuskanta a yake-yaken duniya guda biyu da suka wakana. A kuma halin da ake ciki yanzu haka kasashe 190 ne ke da hannu a wannan yarjejeniya, wacce daga cikin shikashikanta har da daukar nagartattun matakai na kare lafiyar farar fula. A lokacin da yake bayani game da haka Florian Westfal, kakakin Kwamitin Red Cross na kasa-da-kasa dake Geneva cewa yayi:

Alhakin kare lafiyar farar fula ya rataya ne akan dukkan sassan dake da hannun a yakin. Wajibi ne akansu, a karkashin yarjejeniyar Geneva, su rika banbantawa tsakanin bangaren soja da na farar fula a hare-haren da suke kaiwa, su ba da kafar kai taimakon jinkai ga farar fula a dukkan yankunan da ake gwabza yaki a cikinsu.

An sha nanata ambaton yarjejeniyar Geneva ta hudu dangane da yakin Iraki. Amma a game da tabargazar azabtar da fursinoni da sojojin Amurka da na Birtaniya suka yi kuwa, abu ne da ya shafi yarjejeniyar Geneva ta uku, wacce ta tanadi ma’amalla da fursinonin yaki. A karkashin wannan yarjejeniya wajibi ne a mutunta fursinonin yakin a kuma girmama hakkinsu. An haramta kisa ko azabtarwa ko cin mutunci ko kuma gurgunta wani bangare na gabobinsu. Bai kamata a bajesu a bai’nar jama’a tamkar wata haja ta sayarwa ba. Kazalika ba a amince da a dauki hotunan fursinonin domin yayata su a bainar jama’a ba. Yarjejeniyar ta hada har da irin muhallin da ya cancanta a yi musu tare da fayyacewa dalla-dalla a game da ko wane ne fursinan yaki. Kwamitin Red Cross na kasa-da-kasa shi ne ke sa ido akan aikin yarjejeniyar. Ya kan yi amfani da matakai na diplomasiyya domin bin bahasin al’amurra a dukkan yankunan da ake fama da rikici a cikinsu. Kwamitin na Red Cross na da cikakken ikon kai ziyara ga fursinonin domin ganin halin da suke ciki. Sai dai kuma ba kasafai ba ne yake fito da bayanansa a fili sai idan zarafi ya kama. Bugu da kari kuma kwamitin ba ya da wani iko na zartaswa, kamar yadda Westfal ya kara da bayani, inda yake cewar:

A hakika dai kwamitin wata kungiya ce ta taimakon jinkai kuma ba zata iya amfani da karfin hatsi domin tilasta wa sassa dake gwabza yaki su yi biyayya da dokokin da aka tanada ba. Kwamitin bai da ikon hukunta kowa. Wannan alhaki ne da ya rataya wuyan kotunan kasashen da lamarin ya shafa, kamar yadda yake kunshe a kundin yarjejeniyar Geneva."

A hakika kuwa an lura da gibin take tattare da tsare-tsaren dokoki na cikin gida wajen hukunta masu laifukan keta haddin dan-Adam a lokacin yaki. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka kirkiro kutun nan ta kasa da kasa akan masu irin wadannan laifuka. Sai dai abin takaici kotun ba zata iya hukunta sojojin Amurka ba saboda kasar ba ta amince da wanzuwarta ba.