Yarjejeniyar dakatar da buda wuta a birnin Aleppo | Labarai | DW | 05.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar dakatar da buda wuta a birnin Aleppo

Kura ta lafa a wannan Alhamis din a birnin Aleppo na kasar Siriya bayan da yarjejeniyar tsagaita buda wuta da aka tattauna tsakanin Amirka da Rasha ta soma aiki.

Syrien Krieg Kämpfe in Aleppo

Wani titin birnin Aleppo na Siriya

Yarjejeniyar tsagaita buda wutar dai ta zo ne bayan da aka shafe makonni biyu ana fafatawa tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar. Kafofin yada labaran Siriya dai sun sanar cewa, rundunar sojojin kasar ta sha alwashin yin biyayya ga yarjejeniyar ta kwanaki biyu, wadda ta soma aiki da misalin karfe daya na dare.

Mutane da dama dai sun fito bisa titunan birnin na Aleppo, inda shaguna da dama suka buda. Sai dai ana cigaba da fada a wasu yankunan kasar, inda wani dan kunar bakin wake da ya tashi bam din da ke jikinsa, ya hallaka mutane shida a wani kauye da ke gabashin birnin Homs, inda mayakan kungiyar IS ke tada kayar baya.