Yarjejeniya tsakanin ɗarikun Irak | Labarai | DW | 27.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniya tsakanin ɗarikun Irak

Shugabanin ɗarikun schi´a da na sunni, da kuma yan ƙabilar ƙurdawa sun cimma yarjejeniyar komawa kann tebrin shawarwari, da zumar tsaidata wuta, a rikicin da ya ƙi ci, ya ƙi cenyewa a ƙasar Irak.

Sanarwar da fadar shugaban ƙasa, Jallal Talabani ta fiddo, ta bayyana matakan da wannnan yarjejeniya ta cimma daidaito a a kansu, wanda su ka haɗa da cire takunkumi da a ka sakawa magoya bayan tsofuwar jama´iyar Baas ta mirganyi Saddam Hussain,ta fannin harakokin mulki, da kuma shirya zaɓen yan majalisar jihohi.

Kazalika, yarjejeniyar, ta tanadi gama ƙarfi tsakanin ɗariku da ƙabilun Irak, domin kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da ke ci gaba da ɗaiɗaita ƙasar.

Ba da wata wata ba, ƙasar Amurika ta maida martani ga wannan mataki, wanda ta danganta da kyaukyawan sakamako, a yunƙurin samar da zaman lahia mai ɗorewa a Irak.

Wannan saban mataki ya zo, a daidai lokacin da Praminsita Nuri Al Maliki, ke fuskantar matsin lamba na yin murabus daga muƙamin sa.