Yar´adua na ci gaba da ziyara kasashen Africa | Labarai | DW | 09.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yar´adua na ci gaba da ziyara kasashen Africa

Shugaban Nigeriya mai jiran gado, Alh Umaru Musa yar´adua yace yana cike da fatan yan adawa a Nigeria, zasu yi aiki kafada da kafada da gwamnatin sa don ciyar da kasar gaba.

Alhaji Yar´adua ya fadi hakan ne a birnin Firitoria na Africa ta kudu aci gaba da ziyarar kasashen Africa da yake.

Kamfanin dillancin labaru na Africa ta kudu, wato SAPA ya rawaito Yar´adua na cewa tuni ya mika goron gayyata ga jam´iyyun adawa na kasar, don hada karfi da karfe guri guda da nufin yin aiki tare.

Alhaji yar´adua ya shaidawa yan jaridu cewa da alama kwalliya zata biya kudin sabulu a game da wannan mataki daya dauka.

Yar´adua mai shekaru 65, ya kara da cewa gwamnatin da zai kafa nan ba da dadewa na da kyakyawan tsari da shiri na inganta rayuwar yan kasar ta fannoni daban daban na rayuwar bil ´adama.

Kafin dai isar shugaban mai jiran gano Africa ta kudu, ya ziyarci kasashe irin su Togo da Benin da Niger da da kuma Senegal.