Yara nada muhimmanci a tsakanin al´umma.. | Labarai | DW | 25.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yara nada muhimmanci a tsakanin al´umma..

Shugabannin Kiristoci a Jamus, sunyi kiran al´umman Duniya taimakawa gajiyayyu, musanmamma yara ƙanana. Hakan nada nasaba ne da yawaitar rahotanni, na yadda ake take haƙƙokin yara ƙanana ne a Jamus. Shugaban ɗariƙar Protestant a Jamus, Wolfgang Huber, cewa ya yi ranar haihuwar Annabi Isa (As) wato Yesu, ranace dake tunawa bil adama, muhimmancin yara ƙanana, a hannu ɗaya kuma da irin kulawar daya kamata a basu. Shi kuwa shugaban ɗarikar Katolika na Jamus, Cardinal Lehman, janyo hankulan ´yan adam ya yi, wajen yin adalci a tsakanin su, ta hanyar mutuntu juna da kuma tausayawa na ƙasa da su.