Yara masu kirkirar manhaja a Habasha
March 30, 2016Su dai wadannan tsaffin daliban kasar Jamus Amanuel Abraha da Eskinda Momo, sun kadamar da kamfanin mai suna Ahdoo Tec a tsakiyar babban birnin Habasha wato Addis Ababa. Kamfanin na sarrafa sabbin manhaja ga wayoyin salula da ke tallafa wa daliban wajen samun saukin karatu a duk inda suke a kowane lokaci kamar yadda Eskinda Momo ke cewa:
"Fidel dandalin koyon ilimin aiki da yanar gizo ne da wayar salula, wanda zai ba wa dalibai damar samun karatu ta amfani da wayoyin salula, da na'urar tablet ko komfutar tafi da gidanka a duk lokacin da kake so."
A yanzu dai fatan Amanuel Abraha da Eskinder Momo, shi ne manhajar ta kai ga matasan kasar kashi 40 cikin dari da ke samun karin ilmi mai zurfi, kamar yadda Amanuel Abraha ke cewa:
"Karatu a Jamus zai baka damar koyo da kayan aiki masu nagarta kirar Jamus. Sanin kowa ne dai Jamusawa na yin komai cikin inganci da karko."
To sai dai acewar abokinsa Eskinder Momo, kasar Jamus ma na iya amfana da kirkirar 'yan Afirka:
"A tunanina Jamus na iya daukar darusan abubuwa da dama daga Habasha. Babban abin dai shi ne fahimtar juna, ba wai a rika yin abu iri guda a kullum ba."
A yanzu dai, rashin wadatacciyar wutar lantarki da yanar gizo mai karfi, shi ne babban kalubale da ke hana 'yan Habashan cin moriyar irin manhajar yadda ya dace.
'Kimanin dalibai 500 ne ke amfani da manhajar ta Fidel a kan komfuta, to amma Nati Gossaye na cikin masu aiki da manhajar ta wayar salula.
"A kwai jerin darusa cikin manhajar da zai baka dama ka amfana. Zaka iya saukar da nau'uka da dama ko baka da intanet misali darusan lissafi da sauransu."