1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yara 185 ne suka mutu sakamakon cutar baƙon dauro a nahiyar Afirka

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙasashen Afirka 16 ne suka yi fama da baƙon dauro a bana

default

Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ta bayyana ɓullar cutar baƙon dauro a wasu ƙasashe 16 dake yankin tsakiya da kuma yammacin Afirka a bana. Hukumar ta ce mutane 185 ne suka mutu sakamakon cutar daga cikin adadin mutane dubu 22 da suka kamu.

Hukumar ta UNICEF ta ƙara da cewar a yanzu tana da giɓin kuɗi dalar Amirka miliyan 16 daga cikin kasafin data warewa gangamin yaƙi da cutar baƙon dauro a nahiyar ta Afirka, tana mai cewar galibin ƙasashen tsakiya da kuma yammacin Afirka sun ƙaddamar da allurar rigakafi ga ƙasa da kashi 80 cikin 100 na al'ummomin su. Fiye da mutane 400 ne kuma suka mutu a bara saboda matsalar cutar. Ƙasashen yammacin duniya dai sun yi nasarar kawar da cutar amma har yanzu tana ci gaba da zama matsala a ƙasashen dake fama da talauci, inda take yin sanadiyyar mutuwar kusan kashi 30 cikin 100 na yawan ƙananan yaran da suka harbu da cutar - musamman ma waɗanda garkuwar jikin su ke da rauni sosai.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou