Yansanda sun watsar da taron yan adawa a Kampala | Labarai | DW | 18.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yansanda sun watsar da taron yan adawa a Kampala

Jamian yansanda a birnin Kamfala sunyi amfani da karnuka da barkonon tsohuwa ,wajen tarwatsa taron yan adawa,inji shugaban jamiyyar dake kasar Uganda.Kizza Besigye,wanda ke jagorantar gamayyar jammiiyun adawa na Uganda,watau FDC yace an tarwatsa wannan taro nasu nayau dake da nufin kaddamar sabbin katuna wa membobinta.Besigye ya bayyana wannan halayya na jamian tsaron kasar da kasancewa mummunan yunkuri ne na tozartawa magoya bayan jamiyyarsa.To sai dai baa samu jin ta bakin yansandan adangane da wannan rikici ba.Sai dai kaksakin yansanda Robert Kabushenga ya fadawa manema labaru cewa yan adawan basu nemi izinin gudanar da wannan taro nasu ba,kuman an gargadesu dangane da gudanarwa,domin idan sukayi ya sabawa doka.