Yansanda su kashe fursunoni a Iraqi | Labarai | DW | 28.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yansanda su kashe fursunoni a Iraqi

Iraq/police

Yansandan Iraqi sun harbe fursunoni da dama a wata musayar wuta da ta barke a wani kurkukun wani sansanin soji dake Bagadaza.

Rahotanni sunce batakashin dai ta barke ne bayanda wani danfursana ya kwace bindiga daga hannun wani maigadi.

Kawo yanzu dai babu tabbas game da ainahin yawanmutanen da lamarin ya rutsa dasu.

Yayinda yansanda da maaikatar cikin gida na Iraqin sukace samada tsararru ashirinne aka harbe wani jamii yace mutane goma sha biyar kawai lamarin ya rutsa dasu ciki harda wani dansanda da ya rasa ransa wasu daga cikinsu kuwa raunuka kawai sukaji.