Yankin Ossentia na Georgia na son ballewa | Labarai | DW | 12.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yankin Ossentia na Georgia na son ballewa

A yau ne kudancin Ossentia dake son ballewa daga kasar Georgia, ke gudanar da kuri´ar raba gardama, a game da fafutikar da yankin keyi na samun yancin cin gashin kann sa.

Yankin dai na Ossentia ya dade yana wannan fafutika, to amma har yanzu ya rasa samun goyon bayan dangantakar kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu dai tuni, mahukuntan na Georgia suka yi Allah wadai da wannan mataki na kuri´ar raba gardamar da cewa ya kaucewa tsarin doka.

Rahotanni dai sun rawaito mahukuntan na Georgia na cin alwashin dawo da yankin karkashin ikon sa nan bada dadewa ba.

To sai dai a waje daya mahukuntan Russia sun fito fili sun goyi da bayan wannan mataki da yankin na Ossentia ya dauka, tare da mika goron gayyatar zama yan kasar ta Russia gada yawa daga cikin mutanen yankin.