Yankin Kamaru mai amfani da Faransanci yayi bikin mulkin kai | Labarai | DW | 01.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yankin Kamaru mai amfani da Faransanci yayi bikin mulkin kai

Cameroon/Independence

A yaune a yankin kasar kamaru mai amfani da harshen turancin Faranshi akayi bikin shekaru arbain da shida da samun yancin yankin.

Dimbin jamaane dai su ka share saoi da dama suna kade kade da raye raye na bikin murnar zagayowar ranar.

Babban abinda yafi maida hankali akansa a wurin bikin yayin jawabinsa shugaban kasar Paul Biya, shine batun yafewa kasar bashi da kasar ba ta ci gajiyar sa ba kamar yanda sauran takwarorin ta na Afrika suka ci.