Yankin Kahon Afirka na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa | Labarai | DW | 07.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yankin Kahon Afirka na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar miliyoyin mutane a yankin kahon Afirka na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa sakamakon farin da ake fama da shi a wannan yanki. A cikin wata sanarwa da ta bayar kungiyar abinci da aikin noma ta MDD ta kiyasce cewar mutane kimanin miliyan 11 a kasashen Somalia, Kenya, Djibouti da kuma Habasha na bukatar taimakon abinci cikin gaggawa. Hakazalika ana bukatar ruwan sha dabbobi da kuma sabbin iri. Kungiyar ta ce ta fara wannan yekuwa ne a yanzu saboda an shiga lokacin rani kuma ba´a san ran cewa damina bana a cikin watannin maris da afrilu zata yi kyau.