Yankin GTT na cikin wani hali na tsaka mai wuya | Labarai | DW | 09.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yankin GTT na cikin wani hali na tsaka mai wuya

Sarki Abdullah na Saudiyya ya bude taron shekara shekara na shugabannin kasashen yankin Gulf tare da yin gargadin cewa duniyar Larabawa kamar wata gangar hoda ce dake jiran ta yi bindiga. Sarkin ya ba da misali da halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa da Iarqi da kuma Lebanon. Ya ce Falasdinawa na cikin ukuba da wahalhalu na mamaye da Isra´ila ke yi musu amma gamaiyar kasa da kasa ta kasa yin wani abu na kawo karshen wannan bala´i. Sarki Abdullah ya ce abu mafi muni shi ne yadda ´yan´uwa ke zubar da jinin junansu, inda ya yi nuni da rashin jituwar tsakanin kungiyar Fatah da Hamas wanda ke kawo cikas ga kokarin da ake yi na kafa gwamnatin hadin kan kasa. A Iraqi ma har yanzu ´yan´uwa ke yiwa junansu kisan gilla, inji Sarki a jawabinsa na bude taron na yini biyu a birnin Riyadh. Sarkin ya ce Libanon ma na fuskantar baranazar fadawa cikin wani rikicin kabilanci.