1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin 'Yan Jarida

June 13, 2006

A wasu kasashen dake halartar gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ana take 'yancin 'yan jarida

https://p.dw.com/p/Btzj
Kungiyar Togo
Kungiyar TogoHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Duk da kai ruwa ranar da aka sha famar yi dangane da irin ihsanin da za a yi wa ‘yan wasan kasar Togo da kuma barazanar da mai koyar da ‘yan wasan Otto Pfister yayi na janyewa daga bakin aikinsa, amma duk da haka illahirin al’umar kasar ta yammacin Afurka, abin da ya hada har da masu zaman hijira daga cikinsu, na doki da murnar cancantar da kungiyar kwallon kafa ta kasar tayi domin shiga wannan gagarumin biki na kasa da kasa a karo na farko a cikin tarihinta. Misali Ali Tchassanti, dan jarida daga kasar Togo, wanda yayi shekara da shekaru yana zama a garin Wuppertal, sai da ya bude shafi na musamman a yanar gizo domin shirya wa magoya bayan kungiyar wasan Togo gidajen otel masu rafusan farashi yana mai watsi da wasu matsaloli na cin gida. Ali Tchassanti ya ce:

“Maganar ta shafi su kansu ‘yan wasan ne, wadanda ke wa kasarmu wasa. Dukkanmu muna goya musu baya.”

Akasarin al’umar Togo na da irin wannan tutani na Ali Tchassanti. Gasar ta cin kofin kwallon kafa ta taimaka aka samu kusantar juna tsakaninsu suna masu watsi da matsalolin da ake fama da su a kasar abin da ya hada har da take hakkin ‘yan jarida.

“Tun watanni da dama da suka wuce gwamnati ke bakin kokarinta wajen dawo da martabarta a idanun duniya. Yau kimanin watanni 13 ke nan ba tare da mun fuskanci wata matsala ta take ‘yancin ‘yan jarida ba. Mun yi imanin cewar gwamnati na wannan sassauci ne sakamakon gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. Amma fa sanin kowa ne cewar ‘yan jaridar ba su da ikon bayyana ra’ayinsu a fili.”

Ita ma kasar Mexiko daga yankin Latin Amurka dake halartar gasar ta cin kofin kwallon kafa ta duniya ana zarginta da take hakkin ‘yan jarida. An dai saurara daga bakin Katrin Evers daga kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa tana mai cewar:

“Kasar Mexiko ta fi kowace kasa ta yankin Latin Amurka barazana ga ‘yan jarida. Tuni aka yi wa ‘yan jarida biyu kisan gilla a kasar ta Mexiko a wannan shekarar. Kazalika a bara sai da aka kashe wasu ‘yan jaridan guda biyu, a yayinda wani dayan kuma ba a san makomarsa ba tun misalin watanni goma sha biyu da suka wuce.”