′Yancin ′Yan Jarida A Duniya | Siyasa | DW | 26.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yancin 'Yan Jarida A Duniya

Kasashe masu tarin yawa ne ke take 'yancin 'yan jarida a sassa dabam-dabam na duniya

Dukkan dan-Adam na da cikakken hakkin fadin albarkacin bakinsa da kuma neman cikakkun bayanai da rahotanni ba tare da tsangwama ba. Wannan shi ne abin da babi na biyar na daftarin tsarin mulkin Jamus da aka gabatar a shekarar 1949 ya kunsa. A can Amurka kuwa tun a shekarar 1791 aka tabbatar da ‚yancin ‚yan jarida a kundin tsarin mulkin kasar, kazalika a kasar Faransa, ko da yake an dakatar da aikin wannan kuduri a Faransar har tsawon kusan shekaru dari, kafin a sake gabatar da shi. A dukkan kasashen yammaci dake bin tsarin mulkin demokradiyya tsantsan an shigar da kudurin girmama ‚yancin ‚yan jarida a kundayen mulkinsu. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar wadannan kasashen sune akan gaba a cikin jerin kasashen dake girmama hakkin ‚yan jarida, kamar yadda yake a cikin rahoton kungiyar ‚yan jarida ta kasa da kasa. Kasashe bakwai na nahiyar Turai ke cikin jerin kasashe 20 da aka ware domin yaba musu a game da manufofinsu na girmama ‚yancin ‚yan jarida. Su kuwa kasashe irinsu Koriya ta Arewa da Cuba da Burma da Turkmenistan da Eritriya da China da Vietnam suna can gaba-gaba a tsakanin kasashen dake sa kafa suna take hakkin ‚yan jarida. Akwai kasashe da dama a sassa dabam-dabam na duniya, wadanda ‚yancin ‚yan jarida ba ya da wata ma’ana a garesu. Babban dalili kuwa shi ne kasancewar kasashen basa bin tsarin mulki na demokradiyya, sai dai tsarin mulki na kama karya a karkashin wata gwamnati ta tsakiya. A baya ga haka, a kasashen da ake fama da yamutsi a cikinsu, irinsu Afghanistan da Iraki, inda gwamnati ba ta da wani takamaiman angizo, a nan ma maganar ‚yancin ‚yan jarida ba ta taso ba. A rukunin na uku kuwa su ne kasashen dake fama da yake-yake na basasa. A wadannan kasashe babu wani banbanci tsakanin magoya baya da masu adawa da tafarkin demokradiyya. Kowane bangare daga cikinsu kan yi amfani da maganar tsaro domin tace rahotanni kuma duk wanda yayi kurarin saka ayar tambaya akan wannan kuduri zai dandani kudarsa. An fuskanci wannan matsala dangane da yakin tsuburan Falkland da yakin Iraki da kuma yankunan dake karkashin mamayen Isra’ila. Amma fa duk da wannan matsala, akwai masu dagewa wajen ganin lalle sai sun tsage wa jama’a gaskiya ko da kuwa zasu fuskanci barazana ne dangane da makomar rayuwarsu. Babu dai wanda ya san ta inda za a iya billo wa matsalar. Ita kungiyar ‚yan jarida ta kasa da kasa ta kan raba samfurin rigunan nan masu garkuwar harsasai ga manema labarai dake gabatar da rahotanni daga yankunan da ake fama da yaki a cikinsu, amma ba ta da wani iko na dakatar da matakan danne ‚yancin ‚yan jarida. Abu daya da ka taimaka shi ne matsin kaimi daga kasashen demokradiyya da bin diddigin ayyukan ‚yan jarida a kasashen da lamarin ya shafa. To sai dai kuma wannan ‚yancin ba ya nufin ba da ikon fallasa asirin daidaikun mutane masu zaman kansu, kamar yadda ake fama da tafka mahawara akan haka a nan Jamus.