1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

130910 Albuquerque Menschenrechtsrat kurz

Usman ShehuSeptember 19, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya tace samun ruwa sha mai tsabta, yanci ne na ko wane bil'adama

https://p.dw.com/p/PC41
Wani Yaro ke ɗiban ruwaHoto: AP

Samun tsabtataccen ruwan sha dai wani yanci ne da dukkan bil'adama ke da shi a rayuwansa. Kasancewa izuwa yanzu biliyoyin mutane basu kai ga samun wadataccen ruwa ba, shi yasa hukumar kare haƙƙin bil'adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa wani kwamiti na musamman don tabbatar da an aiwatar da ƙudurin.

Bisa ga ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi, dolene a samarwa ko wane bil'adama tsabtataccen ruwan sha bawai a gida kaɗai ba, harma da wuraren aiki da makarantu, wato dai a duk wasu ma'amalolinsu na yau da kullum. Kamar yadda Catarina Albuquerque jami'a ta musamman wajen tabbatar da wannan ƙudurin samar da yancin bil'adama ta fannin ruwan sha ta bayyana

Catarina de Albuquerque
Catarina de Albuquerque.Hoto: Inga Winkler

Tace "Idan baka da lafiya ba zaka je makaranta ba, kuma ba za ka je aiki ba"

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙyasta cewa aƙƙala mutane miliyan 884 ne a duniya basa samu tsabtataccen ruwan sha. Wato ruɓi uku na yawan waɗanda basa da halin samun ingantattun wuraren ba haya. Wannan wata babbar barazanace kamar yadda jakadan ƙasar Boliviya a Majalisar Ɗinkin Duniya ke cewa.

"Rashin tsabtataccen ruwan sha shi ke jawo cututtuka, fiye da wanɗanda yaƙi ke haddasawa. Gudawa shine abu na biyu dake sanadin mutuwar yara 'yan ƙasa da shekaru biyar. Rashin ruwan sha mai tsabta yana haddasa mutuwar yara fiye da in ka haɗa cutar AIDS da maleriya baki ɗayansu".

Talauci na daga cikin abin da ke hana samar da wannan ƙudurin, amma ƙwararrun Majalisar ɗinkin Duniya sukace da farko abinda yakamata a yi shine a gina wuraren ba haya wadatattu, ko da kuwa a yankuna dake da Sahara ana iya samarda hakan, kamar yadda jami'a ta musamman wajen tabbatar da wannan ƙudurin samar da yancin bil'adama ta fannin ruwan sha ta yi misali da ƙasar Masar.

"Basu da ruwa wani makeken Sahara ne kwai ke shinfiɗe, amma duk da haka sun samarwa al'ummarsu ruwan sha, hakan bawai ina nufin sun samarwa kowa ruwan da ta wada ce shi ba, amma dai ko wa yana samun ruwa. Kimanin kashi 70 cikin ɗari na adadin ruwan da ake samarwa ana, yayinda ake amfani da kashi 20 na ruwa ta fannin masana'antu, inda saura kashi goma ake sarrafa shi a al'amuran yau da kullum"

Wasser in Indien Frau am Fluss
Wata mace da 'ya'yanta ke ɗimban ruwaHoto: AP

Yan zu abinda yakamata shine hukumomi su samar da ababen mure rayuwa bawai ga man'yan birane da anguwannin masu hanu da shuni kawai ba. Domin Majalisar Ɗinkin Duniya tace, idan babu wadataccen ruwan sha da tsabtatattun mahalli, to babu yadda za'a samar wa bil'adama yancinsa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal