1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar tserewa daga Boko Haram

Muntaqa Ahiwa / LMJMay 31, 2016

Wata 'yar garin Madagali da ke Arewacin jihar Adamawa a Tarayyar Najeriya da ta tsere daga hannun 'yan Boko Haram, ta bayyana halin kunci da kuma azaba da mata ke fuskanta a dajin Sambisa.

https://p.dw.com/p/1Ixxh
Christina Ijabla da ta tsere daga Boko Haram
Christina Ijabla da ta tsere daga Boko HaramHoto: DW/J.P. Scholz

Matashiyar mai suna Christina Ijabla ta tattauna da wakilinmu na Yola a jihar Adamawa Muntaqa Ahiwa inda cikin hirarsu, ta nuna damuwa kan yadda aka fi mayar da hankali kan 'yan matan makarantar sakandaren garin Chibok na jihar Borno da Boko Haram din suka sace sama da shekaru biyun da suka gabata. Ijabla ta ce akwai daruruwan mata da maza dama kananan yara da har yanzu suke hannun wadannan mayaka.

'Yan matan Chibok da Boko Haram suka sace
'Yan matan Chibok da Boko Haram suka saceHoto: Reuters

Ijabla mai shekaru 20 a duniya na dauke da juna biyu kuma tana gab da haihuwa, an yi garkuwa da ita da ma wasu da dama ne kusan shekaru biyun da suka gabata lokacin da mayakan Boko Haram suka karbe garin Madagali. Ijabla dai ta kubuto daga dajin Sambisa ne makwanni uku da suka gabata. Ta kuma bayyana halin da mata ke ciki a dajin Sabisa da ake tsare da su, musamman auren dole da ake musu.

Auren dole da rashin abinci

Tace: "Abin ci ma babu kuma muna zama ne a karkashin bishiyoyi, suna kuma tsananta mana. Sun ce duk wadda ba za ta yi aure ba, za su yanka ta sai daya daga cikinmu ta ce ba za ta yi auren ba, a gabanmu sai suka ce bari mu gwada muku cewar mu ne ke iko da ku. Sai suka kama yarinyar suka dake ta suka kuma bata kwanaki uku, bayan kwanankin sai suka dawo suka ce ku kuma sauran fa me kuka ce da maganar auren? Sai muka ce sai abin da suka ce, saboda bamu da ikon kanmu. Daga nan sai suka kama yarinyar da ta kin, suka daure fuskarta suka kuma kashe ta, ta hanyar harbin ta da bindiga. Sai suka ce da mu kun dai ga yadda muka yi da ‘yar uwarku, to idan kuka ki hakan zamu yi da ku. Ba mu ganinsu da rana sai dare za su zo kanmu, kuma idan suka zo don kwanciya da mu, sai sun dake mu tukuna."


Christina Ijabla ta kuma yi karin haske dangane da yadda suke da 'yan matan makarantar Chibok a sansanin na Sambisa tana mai cewa:

Daya daga cikin 'yan matan Chibok da ta tsere ta gana da Shugaba Muhammadu Buhari
Daya daga cikin 'yan matan Chibok da ta tsere ta gana da Shugaba Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Halin da 'yan matan Chibok ke ciki

"Kafin a kai mu dai 'yan matan Chibok suna dajin. Sai aka ce mana wadancan ma 'yan matan Chibok ne, sai na ce ‘yan matan Chibok? Zan sami damar magana da su? Suka ce a a, sai dai ganin juna ba dai magana ba. Na bada gaskiya 'yan matan Chibok na raye, suna fama cikin wani hali da sai Allah ne zai fidda su. Wasun su sun yi aure sun haifa 'ya'ya a can, wasu sun rasa rayukansu wasu kuma suna nan dai suna fama a dajin. Sannan bayan su 'yan matan Chibok ma akwai mata da yara da dama, yawancin ma yara kananan ma suna cikin wahala."

Ko ya ya Christina Ijabla ke ji dangane da yadda aka fi fifita batun kama 'yan matan Chibok alhalin kuma akwai 'yan mata da mata da ma yara kanana masu yawa da ke hannun mayakan na Boko Haram a wannan dajin?

Ta ce: "Ni dai babu abin da zan iya fadi, don an damu da 'yan matan Chibok ba damu da saura ba. Ni dai addu'ar da zan yi, kamar yadda na fito Allah ya fitar da su, da ma 'yan matan na Chibok."

Binciken likitoci a Yola, ya gano Christina Ijabla da matsaloli na lafiya musamman karancin jini da rashin abinci a wannan yanayi nata mai bukatar kulawar gaske.