Yanayin bayan zaɓe a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango | Siyasa | DW | 01.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yanayin bayan zaɓe a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango

Bayan zaɓen da aka gudanar a ƙasar Kwango a ran 30 ga watan Yuli, jama'a na nan na ta jiran sakamakon zaben. To ko yaya al'umman ƙasar ke ganin wannan zaɓen? Wai shin an yi shi ne da adallci, ko kuwa an tabka maguɗi? 'Yan kasar dai sun bayyana ra'ayoyinsu da dama a kan waɗannan tambayoyin.

Layin masu ka da kuri'u a ƙasar Kwango

Layin masu ka da kuri'u a ƙasar Kwango

Makarantar sakandare ta Lycée Molière da ke birnin Kinshasa, na ɗaya daga cikin cibiyoyin zaɓe a birnin. A nan ne kuma Caroline Itussi ta ka da ƙuri’arta a karo na farko a rayuwarta, a ranar lahadin da ta wuce. Jama’a da dama, kamar dai Caroline Itussin sun sake dawowa a makarantar, don su gano wa idanunsu, yadda ake gudanad da ƙidayar takardun zaɓen. Game da tambayar ko yaya take ɗaukar wannan zaɓen da aka gudanar a ƙasarta, Caroline Itussi, ta bayyana cewa:-

„Na gamsu ƙwarai, kuma na tabbatar cewa, wannan zaɓen na da muhimmanci. Idan a ko’ina haka yanayin zaɓen ya kasance, to za mu iya yin fara’a da hakan. Shirya irin wannan zaɓen dai shi ne karo na farko a nan ƙasar. Yannzu an gama lami lafiya, kuma hankalin kowa a kwance yake. Muna dai yi wa masu shirya zaɓen matuƙar godiya, game da yadda suka tafiyar da aikinsu.“

Richard Kaboya, na ɗaya daga cikin jami’an kula da ganin cewa an bi tsarin zaɓen bisa ƙa’ida. Zai dai kasance a gun zaɓen ne har zuwa lokacin da aka gama ƙirga ƙuri’un tukuna. Shi ma ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaen ya gudana, amma yana kuma mai suka ga tsarin aikinsu:-

„Ɗimbin yawan jama’a ne suka zo ka da ƙuri’unsu. Amma inda sukar da zan yi ga tsarin aikinmu. Kwana uku kawai muka yi taron bita, kuma tun wannan lokacin ba a biya mu ko kwabo ba. To mu dai masu kishin ƙasa ne, muna wannan aikin ne saboda ci gaban ƙasarmu. Duk da illolin da muke huskanta, muna dai ƙoƙarin ba da gudummowarmu ga cin nasarar shirya wannan zaɓen, saboda nan gaba, kamar yadda muke fata, a sami jami’an da ke wakilcin al’umman ƙasar nan, kuma waɗanda suka sa bukatun al’umman a zukatansu.“

Ba dai a ko’ina ne jama’a suka bayyana gamsuwarsu ga yadda aka gudanar da zaɓen ba. Kamar Lievin Panzu, jama’a da dama kuma sun yi koke-koke game da abin da suke gani kamar maguɗi a wasu rumfunan zaɓen. Shi dai Panzu, a mazaɓar Kalamu da ke wajen birnin Kinshasa ne ya ka da ƙuri’arsa. Ya dai bayyana ɓacin ransa ne da cewa:-

„Ban gamsu ba ko kaɗan da yadda ababa suka kasance. Akwai maguɗi da yawa. An sami ƙararraki da dama, inda jama’a suka je ka da ƙuri’unsu, amma da suka kai gaban jami’an, sai aka ce musu ai tuni sun jefa ƙuri’un, alhali kuwa, bas u ne suka jefa. Waɗansu aka samo suka jefa ƙuri’un da sunayensu. Wannan dai ba abin alheri ba ne gare mu.“

Haƙiƙan an sha samun irin waɗannan koke-koken. Amma, Ulrich Stockmann, ɗaya daga cikin jami’an sa ido kan zaɓen da Ƙungiyar Haɗin Kan ta tura zuwa Kwangon, ya ƙi ganin hakan tamkar maguɗi. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Babu shakka, akwai ƙananan matsalolin da aka samu, amma waɗannan na da asali ne daga ɗan cikas ɗin da aka samu a tsarin shirye-shiryen zaɓen. A lal misali, akwatunan ka da ƙuri’un sun cika da wuri, saboda girman takardun zaɓen. A nan kuwa, kai tsaye ya kamata a ɗau matakan magance matsalar. Ba za a iya ganin haka tamkar tabka maguɗi ba. Ni dai ba ni da ra’ayin cewa, an yi wani maguɗi a zaɓen.“

To wannan dai ra’ayin mai sa ido ne a zaɓen. Hukumar zaɓen ƙasar, ita ce za ta iya yanke shawara ta ƙarshe kan inganci ko kuma rashin adalci a zaɓen. Amma babu shakka, ababa da dama sun wakana a wasu rumfunan zaɓen, waɗanda ba su dace da tsarin ka da ƙuri’un ba. An sami wurare da dama, inda kai tsaye aka ga cewa rajistar masu zaɓen ta ɓace, ko kuma aka lura da cewa mutane da dama sun yi rajista a mazaɓu daban-daban da canza sunayensu. A wasu mazaɓun kuma, shugabanninsu sun hana masu sa ido shiga rumfunan ka da ƙuri’un. Masu ka da ƙuri’un da dama kuma sun tabbatad da ganin takardun zaɓen da yawa, da tuni aka sanya alamomi a kansu, kafin ma a miƙa musu su.

 • Kwanan wata 01.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyn
 • Kwanan wata 01.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyn