Yanayi: Yarjejeniyar Paris na samun ci-gaba | Labarai | DW | 17.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yanayi: Yarjejeniyar Paris na samun ci-gaba

Ministocin muhalli na kasashe 30 da suka yi wani zama a birnin Montreal na Kanada kan batun yarjejeniyar rage dumamar yanayi, sun samu babban ci-gaba wajen hanyoyin aiwatar da ita.

Kanada Treffen der Umweltminister (Getty Images/AFP/A. Chiche)

Babban zaman tattaunawa a kasar Canada kan batun dumamar yanayi

A lokacin da take magana bayan kammala zaman taron, Ministar muhalli ta Kanada Catherine McKenna, ta ce batun aiwatar da yarjejeniyar babu gudu babu ja da baya:

"Yayin wannan zaman taro namu mun amince da cewa yarjejeniyar da aka cimma a birnin Paris, yarjejeniya ce da ba za a sauya wani abu daga cikinta ba. Duk mun amince da ba da himma wajen aiwatar da yarjejeniyar. Sannan kowa ya amince cewa muhalli da tattalin arziki na tafiya ne tare, domin ba za ka iya tafiyar da harkokin tattalin arziki, ba tare da ka kula da yanayi ba."

Shi ma daga nashi bangare babban Kwamishinan Tarayyar Turai kan batun muhalli da makamashi Miguel Arias Canete, ya ce babban burin da suka sa gaba kan wannan tsari na tsaftace yanayi, na da goyon baya mai muhimmanci daga ko'ina.