Yanar gizo a Saliyo | Siyasa | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yanar gizo a Saliyo

Tun a 1996 kasar Saliyo take amfani da yanar gizo duk da yakin basasar dake addabarta a wancan lokaci

Kasar Saliyo dai har yau, bayan kawo karshen yakin basasarta shekaru biyar da suka wuce, tana cikin rukunin kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu dake fama da mummunan talauci a duniya, duk da taimakon kudi da take samu daga kafofi na kasa da kasa. Wannan matsalar kuwa tana da dangantaka ta kut da kut da fasahar aiwatar da yanar gizo a kasar domin kuwa tana fama da karancin wutar lantarki, kamar yadda aka ji daga James Bognaby dake da shagon na’ura mai kwakwalwa ta internetcafe a garin Bo, wanda shi ne na biyu wajen girma a kasar Saliyo, lokacin da yake kokarin gyara na’urarsa ta janaretor. Bognaby ya ci gaba da cewar:

“Abin dake faruwa shi ne. A hakika muna bukatar janaretoci guda biyu in an kashe wuta. Amma kuma dukkansu biyu sun lalace ta yadda ba zamu iya ci gaba da aiki ba sai bayan mun aiwatar da gyare-gyare akansu.”

Kashe-kashe wutar lantarki dai tuni ya zama ruwan dare a kasar Saliyo. Shi dai Bognaby injiniya ne kuma shi ne shugaban kamfanin da ake kira Access to Africa Punkt Com, wanda shi ne kamfanin intenetcafe mafi girma a yammacin Afurka. A hukumance dai kamfanin na da mazauninsa ne a Amurka saboda manufofin tsaro, amma a hakika shelkwatarsa a Bo take, ta kasar Saliyo. Kamfanin na da Rassa a Nijeriya da Kamaru, sai dai kuma ta fi fama da matsaloli a Saliyo wajen samun ciniki. Bognaby ya ce:

“A gareni, a matsayina na dan kasuwa, mutuwar wutar lantarki babbar asara ce. Abokan ciniki zasu shigo nan kantin amma ba ni da ikon biya musu bukata. Wannan abin bakin ciki ne a gare ni.”

Ita dai yanar gizon tana taka muhimmiyar rawa a harkokin sadarwa tsakanin kasa da kasa, kamar yadda aka ji daga bakin Max Muhammde Kenne shugaban wani shirin taimaka wa manoma a kasar Saliyo karkashin jagorancin kungiyar taimakon fasaha ta Jamus GTZ a takaice. Kenne ya ce:

“Yanar gizon na da dangantaka da aiki na. Ni kann kuma yi amfani da ita domin tuntubar abokan aikina a ketare, hatta a kasashen Afurka, musamman ma cibiyoyin da muke ma’amalla da su. Kazalika ni kann yi amfani da yanar gizon domin tuntubar dangina dake ketare.”