´Yan tawayen Tamil Tigers sun yi barazanar komawa filin daga | Labarai | DW | 13.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan tawayen Tamil Tigers sun yi barazanar komawa filin daga

´Yan tawayen Tamil Tigers a Sri Lanka sun ce zasu koma ga yaki gadan-gadan idan aka hana su shiga cikin tekun kasar. Wannan barazanar ta zo ne kwanaki kadan bayan da ´yan tawayen suka nitsar da wani jirgin ruwan rundunar sojin kasar a wani gumurzu da suka yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Rikicin da ya kunno kaya baya bayan nan tsakanin ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers da gwamnati na barazana ga dorewar wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta da sassan biyu suka cimma a shekara ta 2002. Da farko KTT ta yi gargadin cewa harin da ´yan tawayen suka kai ka iya yin illa ga shawarwarin samar da zaman lafiya da za´a yi a gaba.