Yan tawayen Sudan sun kauracewa tattaunawar sulhu | Labarai | DW | 27.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan tawayen Sudan sun kauracewa tattaunawar sulhu

An fara tattaunawar cimma sulhu kann rikicin yankin Darfur, ba tare da halartar da yawa daga cikin wakilan kungiyoyin yan tawayen ba. Tattaunawar dake gudana a Sirte na kasar Libya, na wanzuwa ne karkashin kungiyyar Mdd da kuma kungiyyar hadin kann kasashen Africa Au.A yanzu haka dai bayanai sunce kungiyyar yan tawaye ta SLM ce kawai ta sami halartar wannan taro.Masu nazarin harkkokin siyasa, a yanzu haka na shakkun cimma wani tudun dafawa a wannan tattaunawa, bisa kauracewar kungiyoyin yan tawayen. Kafafen yada labarai sun rawaito Wakilin Mdd a yankin na Darfur, Jan Ellisson na cewa,matukar ba´a cimma wani abin azo a gani ba a wannan karo, to babu shakka za´a shiga cikin wani hali na rudani. Kungiyoyin yan tawayen dai sun kauracewa tattaunawar ne a cewar bayanai, bisa gaza yin wani abin azo a gani game da rikicin na Darfur daga bangaren Mdd da kuma kungiyyar ta Au.