1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'yan tawayen Philipines sun bada kai

November 29, 2007
https://p.dw.com/p/CUft

Rahotanni sunce an kame sojojin ‘yan tawaye da wasu farraren hula da ke basu goyan baya, lokacin da suka mamaye wani hotel dake birnin Manila a ƙasar philipines. Jami’an tsaro dauke da miyagun makamai suka tursasa ƙeyar ‘yan tawayen da suka bada kai daga sansannin hotel din. Tun da farko sai da ‘yan tawayen suka sanar cewar zasu ba da kai bori ya hau, domin sun tabbatar da kariya ga lafiyar fararen hula da ‘yan jaridu dake tare da su a cikin hotel ɗin. Da yawa daga cikinsu na fuskantar zargi kan shirin junyin mulki a shekara ta 2003. ‘Yan tawayen sun mamaye hotel ɗin ne bayan sun gudo daga harabar kotu inda suke fuskantar ƙara. ‘Yan tawayen dake samun goyan baya daga wasu ‘yan ta’ada na kira ga shugaba Gloria Arroyo da ta sauka daga mulki.