Yan tawayen Nepal sun yi tayin tsagaita wuta | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan tawayen Nepal sun yi tayin tsagaita wuta

Yan tawayen Nepal sun baiyana tsagaita wuta domin raɗin kan su na watanni uku, domin bada dama ga sabuwar gwamnatin da aka kafa ta ƙarbi ragamar gudanarwa cikin kwanciyar hankali. Tun da farko, yan tawayen na Maoist, sun janye togaciyar da suka yi a babban birnin ƙasar Katmandu, bayan da sabon P/M na Nepal G.P. Koirala ya tabbatarwa da alúmar ƙasar cewa zaá gabatar da sabon kundin tsarin mulki bayan an kammala zaɓen majalisun dokoki. A cikin wannan makon ne basaraken Nepal, Sarki Gyanendra ya mayar da tsohuwar majalisar dokokin bayan da jamíyun adawa da ƙungiyoyi masu fafutukar cigaban dimokraɗiya suka gudanar da gagarumar zanga zanga ta gama gari wadda dauki tsawon makwanni biyu ana gudanarwa a ƙasar. Dubban jamaá a ƙasar sun gudanar da taron gangami a Katmandu kusa da fadar sarkin inda suka yi kiran da ya yi murabus ya kuma tattara ya na sa ya na sa ya bar ƙasar.