Yan tawayen Maoist sun halaka mutane 17 a india | Labarai | DW | 27.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan tawayen Maoist sun halaka mutane 17 a india

Yan twayen kungiyyar Maoist a India sun bude wuta kann mai uwa da wabi a cincirindon yan kallo, a wani filin tamaula dake jihar Jharkhand, a gabashin kasar.Hakan a cewar rahotanni ya haifar da asarar rayuka a kalla 17, ban da wasu da dama da suka jikkata.Wani jami´in yan sanda ya shaidar da cewa, yan tawayen kusan 40 dauke da muggan makamai ne suka kutsa kai cikin filin tamaulan, ba kuwa tare da bata lokaci ba suka bude wuta kann yan kallon.Al´amarin a cewar rahotanni ya faru ne a daren jiya, jim kadan bayan kammala wasan tamaulan.