´Yan tawayen LRA a Uganda na cin karensu ba babbaka | Labarai | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan tawayen LRA a Uganda na cin karensu ba babbaka

Babban jami´in dake kula da ayyukan jin kai na MDD Jan Egeland ya bukaci kwamitin sulhu da ya dauki tsauraran matakai akan ´yan tawayen kasar Uganda da suka addabi jama´a a Uganda, Sudan da kuma JDK. Egeland ya ce har yanzu kungiyar Lord´s Ressistance Army wato LRA a takaice ta na samun makamai daga wasu wurare kuma hare haren da take kaiwa sun tilasta mutane kusan miliyan biyu neman mafaka a sansanonin ´yan gudun hijira. Jami´in ya kara da cewa hare haren ´yan tawayen na janyo cikas ga aikin kungiyoyin agaji. Daga tsakiyar watan satumba zuwa yau an kashe fararen hula masu yawan gaske da kuma ma´aikatan agaji 4 sakamakon hare haren ´yan tawayen kungiyar ta LRA. Egeland ya ce har yanzu ´yan tawayen na cin karensu babu babbaka shi ya sa ya zama wajibi kasashen 3 makwabtan juna wato Uganda, Sudan da JDK su kare al´umominsu.