´Yan tawayen FARC a Kolumbia sun saki wasu mata biyu da suka yi garkuwa da su | Labarai | DW | 11.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan tawayen FARC a Kolumbia sun saki wasu mata biyu da suka yi garkuwa da su

Matan nan biyu da aka sako su bayan an shafe shekaru masu yawa ´yan tawayen ƙungiyar FARC a ƙasar Kolumbia suna garkuwa da su, sun isa Venezuela. A birnin Caracas, shugaban Venezuela Hugo Chavez ya tarbi matan biyu da suka haɗa da tsohuwar ´yar majalisar dokoki Consuleo Gonzales da kuma Clara Rojas tsohuwar mai yiwa ´yar takarar shugaban ƙasar Kolumbia Ingrid Betancourt yakin neman zabe. Shugaban Chavez ya shiga tsakani aka saki matan. A cikin watan fabrairun shekara ta 2005´yan yaƙin sunkurun FARC suka sace Rojas da Betancourt. A cikin hirar da aka yi da ita Rojas ta ce shekararta uku rabonta da ganin Betancourt.