’Yan tawayen Darfur sun isa a birnin Khartoum. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

’Yan tawayen Darfur sun isa a birnin Khartoum.

Wata tawagar ’yan tawayen yankin Darfur, ta isa a birnin Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan, a karo na farko tun da ɓangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan jiya a birnin Abujan Najeriya. An dai ɗau tsauraran matakan tsaro a kewayen tawagar ’yan tawayen, wadda ta je birnin don aiwatad da da yarjejeniyar. Har ila yau dai, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ’yan tawayen guda 3 ne ta sanya hannu kan yarjejeniyar, wadda Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU ta jagoranci tsarawa. Sauran ƙungiyoyin biyu sun ce, yarjejeniyar ba ta yi la’akari da bukatunsu ba.

Yarjejeniyar dai ta tanadi kafa wata hukuma ne ta wucin gadi a yankin na Darfur, wadda ƙungiyar SLA da ta sanya hannu a kanta za ta jagoranta. Tawagar ƙungiyar, da ta isa a birnin Khartoum yau, ƙarƙashin shugabancin Minni Arcua Minnawi, z ata sa ido ne kan aiwatad ƙa’idojin yarjejeniyar, waɗanda suka haɗa har da sake gina yankin na yammacin Darfur, da yaƙi ya ragargaza.