′Yan tawayen Chadi sun yi gargadi | Labarai | DW | 29.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen Chadi sun yi gargadi

Chadi/EU

‘Yan tawaye a ƙasar Chadi sun yi gargaɗi cewa zasu yaƙi rundunar da ƙungiyar Tarayyar Turai ko EU, ke shirin turawa zuwa ƙasar, tamkar kamar sojojin mamaye na ƙetare idan har sun nuna alamun goyan bayan shugaba Idris Derby. Gargaɗin na ƙungiyar ‘yan tawayen, ya zo ne bayan wani munmunar bata kashi a gabacin Chadi, wanda ya janyo rugujewar yarjejeniyar tsaigaita wuta na tsawon wata ɗaya da aka cimma. Rikicin ya faru ne kusa da wani sansanni dake bakin iyakar ƙasashen Sudan da Chadi, inda ake shirin yiwa rundunar na EU, su dubu hudu mazauni.