´Yan tawayen Chadi sun nemi bayani daga ministan harkokin wajen Faransa | Labarai | DW | 17.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan tawayen Chadi sun nemi bayani daga ministan harkokin wajen Faransa

´Yan tawayen da ke kokarin kifar da gwamnatin Chadi sun ce sun rubutawa ministan harkokin wajen Faransa Phillippe Douste-Blazy wata wasika inda suka nuna bukatar gudanar da wani taro don tattaunawa akan aikin dakarun Faransa a cikin Chadi. To amma wata mai magana da yawun ma´aikatar harkokin wajen ta ce ba su da wata masaniya game da wannan wasika. A cikin wata sanarwa da suka bayar jiya da daddare ´yan tawayen sun ce suna bukatar bayani akan harbin gargadi da jiragen saman yakin Faransa suka yi akan wani ayarin ´yan tawaye a cikin makon da ya gabata. ´Yan tawayen sun yi kira da a dauki matakai na bai daya don hana yin wani artabu tsakaninsu da dakaru Faransa. Faransa na da dakarun kimanin dubu daya da 200 a Chadi daukacin su a wani barikin soji dake birnin N´djamena.