Yan tawayen Basque sun sanarada ajiye makamansu har abada | Labarai | DW | 22.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan tawayen Basque sun sanarada ajiye makamansu har abada

Kungiyar yan aware ta kabilar Basque ETA a kasar Spaniya ta sanarda tsagaita bude wuta na dindindin wanda tace zai fara aiki a ranar jumaa mai zuwa.

Wannan dai shine matakin farko na shirin wanzar da zaman lafiya bayan tahe tashen hankula na kungiyar,wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 850 tun 1968,a kokarin kungiya na samarda kasa mai cin gashin kanata daga bangaren arewacin Spaniya da kuma kudancin Faransa.

Kungiyar ta ETA wadda Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suka jere ta cikin kungiyoyin yan taadda,tunda da farko ta sanarda tsagaita bude wuta a watan satumba na1998,amma ta janye a 1999.

A yanzu haka kungiyar tace ta kudiri aniyar bin hanyoyin demokradiya wajen cimma burinta bna samarwa yan kabilar Basque kasa mai cin gashin kanta.