1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen ƙasar Tchad na shirin shiga birnin N´Djamena

April 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bv25

A ƙasar Tchadi a na ci gaba da barin wuta, tsakanin yan tawaye da rundunar gwamnati.

Majiyoyin diplomatia a wannan ƙasa sun bayana cewar, ya rage kilimota 40 kurum, yan tawaye su shiga N´Djamena babban birnin ƙasar, to amma da alamun sojoji masu biyayya ga gwamnati, sun taka masu birki.

Wakiliyar kamapanin dullan cinlabarun AFP, ta faɗa cewa, a sahiyar yau, an koma ɓarin wuta tsakanin ɓangarorin 2, gap ga kewayen N´Djamena, inda sojoji masu biyyaya ga gwamnati, su ka kai hari, ga yan tawayen da ke shirin shiga babban birnin.

Kakakin rundunar tawaye a ƙasar France, tsofan ministan harakokin wajen Tchadi, Laona Gong ,ya sanar cewa a halin da ake ciki, rundunar tawayen FUC, na riƙe da kashi 80 bisa 100 na kasar.

Mazamna birnin N´Djamena, wanda a yanzu haka, babu shiga da fita a cikin sa, sun wayi gari cikin halin ɗar -ɗar.

A na kauttata zaton, a fuskanci yaƙe-yaƙe ayau , domin wakilan kamapanin dullacin labarun Reuters, ya tabbatar da cewa, a na jin ƙaran tashin manyan bindigogi daga N´Djamena.

A nasu ɓangaren Amurika, da Majalisar Ɗinkin Dunia, tunni, sun kwashe mafi yawan jami´an su, daga N´Djamena, sannan, da dama daga opisoshin jikadanci sun rufe kofofin su.