1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawaye sun sake kai harin bam a kudancin Nigeria

April 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0C

Sojojin sa kai a Nijeriya sunce sun dana wani bam na cikin mota kusa da matatar mai na Warri dake kudancin kasar.

Kungiyar fafautukar yantar da yankin Niger Delta,wadda hare hare da take kaiwa suka katse yawan mai da Nijeriya ke samarwa a kowace rana tace ta dana bam din ne a tsakiyar tankokin mai a bakin matatar ta warri.

Komandan soji da aka girke suyi maganin yan tawayen,Birgediya Janar Alfred Ilogho,ya tabbatar da kaiwa harin,amma yace babau wanda ya samu rauni,haka kuma sojoji sun kange yankin.

Kungiyar ta yan tawayen Niger Delta,tace wannan hari gargadi ga dukkan maaikatan mai na Nigeria,musamman ma yan kasar Sin.

A farkon wannan mako ne shugaba Hu Jintao na kasar Sind in ya sanya hannu akan yarjejeniyar cikinkin mai da Nigeria a lokacin ziyararsa.