An kai hari a sansanin sojojin Mali
July 19, 2016Talla
Wasu da ake zargi masu jihadi, sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar kasar Mali a birnin Nampala. A cewar magajin wani gari da ke kusa da yankin ya ce "Mayakan sun zo da manyan motoci hudu wasu kuma a kan babura, amma dakarun gwamnatin na sake jan damara a birnin Diabaly dan kwace iko da sansanin."
Kimanin sojoji 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikata a harin. A shekara ta 2013, kasar Faransa ta jibge dakarunta a kasar Mali da nufin fatattakan mayakan da ke yunkurin mamaye arewacin Mali. Ko a kwanan ma an rattaba hannu kan yarjejeniya da wasu 'yan tawayen Mali a Jamhuriyar Nijar da nufin ajiye makamai dan kwantar da tarzoma.