1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawaye sun kai hari kan soji a Kongo

November 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuaU

A kasar Kongo magoya bayan wani janar na soja da yayi tawaye sun kai hari da manyan makamai kan sansanonin soji a gabashin kasar.

Ministan harkokin cikin gida na Kongo Denis Kalume yace dakarun shugaban tawayen janar Laurent Nkunda sun kaddamar da hari a sansanin Sake yau da safen nan,inda dakarun sojin kasar kuma suka maida martani.

Majiyoyi daga MDD sun tabbatar da kaiwa wannan hari a yankin na Sake wanda shinnge ne tsakanin dakarun gwamnati dana yan tawayen.