yan tawaye sun harbo wani karamin jirgin yakin rundunar da makami mai linzami a gabashin kasar . | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

yan tawaye sun harbo wani karamin jirgin yakin rundunar da makami mai linzami a gabashin kasar .

Jamian soji a kasar Chadi sunce yan tawaye sun harbo wani karamin jirgin yakin rundunar da makami mai linzami a gabashin kasar .

Kakakin gwamnati Hourmadji Moussa Doumgour ya fadawa taron manema labari cewa an harbo jirgin ne kusa da bakin iyakar kasar Sudan.

Ya kuma zargi Sudan da goyon bayan yan tawayen.

Sojojin sa kai dai suna anfani da wannan yanki wajen kaddamar da hare hare akan dakarun gwamnati.

Doumgor ya fadawa manema labarai cewa zaa sake tsaurara dokar ta baci kuma sojoji zasu kasance cikin shirin ko ta kwana.

Ya kuma yi kira ga MDD da AU da su kwashe yan gudun hijira na Sudan dake sansanonin bakin iyaka kasar.

Jamiin na Chadi yayi ikrarin cewa wasu daga cikin yan gudun hijirar suna yiwa gwamnatin Sudan aiki don su kawo hargitsi a Chadi.