´Yan tawaye sun halaka sojin Amirka 3 a Afghanistan | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan tawaye sun halaka sojin Amirka 3 a Afghanistan

An kashe sojojin Amirka 3 a gabashin Afghanistan. Rahotanni sun nunar da cewa mayakan Taliban su kaiwa dakarun na Amirka hari a lardin Nuristan a jiya juma´a. A kuma can lardin Kandahar dake kudancin Afghanistan, an halaka sojin Canada daya lokacin da wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan wani ayarin motocin sojojin kawance. Mutuwar sojin ya kawo yawan sojojin Canada da aka kashe a Afghanistan zuwa 7 a cikin mako daya. A wani labarin kuma an halaka mutane 3 da ake zargi mayakan kungiyar al-Qaida ne sannan an tsare wasu 3 a wani samame da sojojin kawance karkashin jagorancin Amirka suka kai a lardin Khost na gabashin Afghanistan.