1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan tawaye a Kolombia sun kai harin kan ´yan sanda

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/Budf
Fiye da mutane 20 sun rigamu gidan gaskiya sannan da dama suka jikata a wani hari da ´yan yakin sunkurun Kolombia suka kai kan wani sansanin ´yan sanda. Kamar yadda hukumomi suka nunar, daga cikin wadanda suka mutu akwai ´yan sanda da ´yan tawaye da kuma fararen hula. Rahotannin sun yi nuni da cewa ´yan tawayen kungiyar FARC su kimanin 70 suka kai hari da bindigogin masu sarrafa kansu da rokoki akan sansanin ´yan sanda dake garin Tierradentro dake can arewacin kasar. Wannan dai shi ne hari mafi muni da ´yan tawayen suka kai tun bayan da shugaban kasa Alvaro Uribe ya dakatar da tattaunawar da ake yi da kungiyar FARC akan yiwuwar yin musayar firsinonin ´yan tawaye da mutanen da ´yan yakin sunkurun ke garkuwa da su.