′Yan Taliban sun kai wani hari a Kabul | Labarai | DW | 01.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Taliban sun kai wani hari a Kabul

Kungiyoyin 'yan ta'addan sun zafafa hare-haren da suke kai kwanakinnan a kasar ta Afganistan abin da ke maida agogo baya bisa shirin zamar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Harin dai ya yi sandiyyar rasa rayuka da kuma jikkata mutane 38, tun da farko dai wasu 'yan kunar bakin wake ne suka afka da mota cikin wani sansani na jami'an tsaro, inda suka dinga musayar wuta a tsakanin su, a daidai lokacin da bom ya tashi da wani dan ta'adda da ke kokarin shiga ofishin leken asiri a gabashin Kabul, babban birnin kasar ta Afganistan. Ya zuwa yanzu dai kakakin kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid, ya rubuta a shafin twitter cewar 'yan kungiyar su ne suka kai harin kuma sun yi shahada.