Yan Taliban sun kai hari akan motocin NATO | Labarai | DW | 06.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Taliban sun kai hari akan motocin NATO

Taliban sun zafafa kai hare hare akan jerin gwanon motocin mai na NATO

default

Tankokin mai da yan Taliban suka cinnawa wuta.

Yan sanda a Pakistan sun ce yan bindiga dadi sun kai hari tare da cinna wuta akan jerin gwanon motocin tankar mai na kungiyar tsaro ta NATO wadanda ke kan hanyar su ta kai man Fetur ga rundunar sojin a Afghanistan a yau Laraba. An ruwaito cewa daya daga cikin direbobin ya rasa ransa. Sai dai kuma kungiyar Taliban ta yi ikrarin cewa ita ce ta kai harin. Wannan dai shine hari na baya bayan nan da aka kai akan jerin gwanon motocin daukar mai a Pakistan. A waje guda dai jami'an gwamnatin Pakistan wadanda suka fusata da kutsen da NATO ke yi a cikin kasar domin kai farmaki sun rufe babbar hanyar da ake safarar kayayyaki zuwa Afghanistan. Ita dai kasar Pakistan tana da matukar muhimmanci ga dakarun tsaron na NATO a yakin da suke yi a Afghanistan.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu