Yan takifen Fatah Al Islam sun yi saranda | Labarai | DW | 02.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan takifen Fatah Al Islam sun yi saranda

Rahottani daga birnin Beyruth na ƙasar Libanon,sun ce ƙura ta lafa,a yankin Nahr Al Bared, bayan fiye da wattani 3 a na gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnati da baraden Fatah Al Islam da su tada bori.

Kakakin rundunar gwamnati ya tabatar da cewa, a halin yanzu sun yi nasara murƙushe wannan bori.

Da dama daga yan takifen sun buƙaci ranta cikin na kare, to saidai sojojin gwamnatin sun capke fiye da 15 daga cikin su, tare kuma da harbe wasun su.

Saidai a yanzu haka, sojojin gwamnati na cigaba da lalube nakiyoyi da yan takifen su ka daddasa a yankin.

Fiye da mutane 200 su ka rasa rayuka, a cikin wannan yaƙi wanda ya fara tun ranar 20 ga watan mayu.

Rundunar gwamnati ta yi asara sojoji 153.

Baki ɗayan mazauna wannan yanki, su kimanin dubu 31 sun ƙaurace masa, tun farkon ɓarkewar rikicin.