Yan takifen Afghanistan sun yi belin bajamushen da su ka yi garkuwa da shi | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan takifen Afghanistan sun yi belin bajamushen da su ka yi garkuwa da shi

Wasu yan takifen Afghanistan, sun yi belin bajamushen nan, da su ka yi garkuwa da shi,makon da ya gabata, a yankin kudu maso yammacin ƙasar.

Opishin Ministan harakokin cikin gida na Afghanistan, ya bada wannan albishir ga kumomin Jamus.

Kakakin ministan, Zemari Bashary, ya tabbatar da cewa, wannan bajamushe na cikin ƙoshin lahia, saidai bai bayyana wanda ke da alhakin kamun ba.

Jim kaɗan kamin belin, Gwamnana jihar Farah inda abunya faru,ya ce yan takifen, sun gitta sharaɗin a biya su diyar dalla dubu 40, kamin sun sake pirsinan

Ƙungiyar yan taliban da gwamnati ta zarga da sace wannan bajamushe, ta mussamanta zargin, ta kuma tsame hanunta daga hare-haren da aka shiryawa da zumar karɓar kuɗaɗen diyya.

A wani ɓangaren kuma na Afghanistan, jami´an tsaro 5 su ka rasa rayuka, da sanhin sahiyar yau, a sakamakon tarwatsewar wata Bam, a opishin yan sanda, na birnin Spin Boldak, gap ga iyaka da Pakistan.