yan takife sun sallami yan jaridar nan 2 na FOx News da su ka kama | Labarai | DW | 27.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

yan takife sun sallami yan jaridar nan 2 na FOx News da su ka kama

Yan takife a zirin Gaza sun sako yan jaridar nan 2, na Fox News ,da su ka kame tun ranar 14 ga watan da mu ke ciki.

An sallami Steve Centani, ɗan kasar Amurika, da Olaf Wiig ɗan New Zeland, bayan sati 2 a cikin hannu yan takifen.

An sake su, jim kaɗan bayan da jaridar Fox News, ta samu faifen videon su, inda su ka ce yanzu sun musulunta.

Bayan sakin da a ka yi masu, ɗaya daga cikin su, wato Steve Centani, ya bayana wa manema labarai cewar, yan takifen sun cilasta masu ne, tuba zuwa addinin Islama.

Ƙungiyar baraden Jihadi, ta bayyana ɗaukar alhakin capke yan jaridar 2, tare da gitta sharaɗin Amurika, ta yi belin pirsinoni musulmi ,da ta ke tsare da su.

Praministan Palestinu Ismail Hanniey, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun belin yan jaridar, ya kuma sanar da cewa ƙungiyar da ta capke su, ba ta da nasaba, da Alqi´da saɓanin yada a ka yi ta yayatawa.