Yan takarta 32 za su shiga zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 06.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan takarta 32 za su shiga zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Jamhuriya demokradiyar Kongo, ta bayyana jerin sunayen yan takara da za su shiga zaɓen shugaban ƙasa.

Hukumar ta amince, da takardun yan takara 32, ta kuma yi watsi da 41.

Yan takarar 32 da za su shiga zaɓen, sun haɗa da mata 3.

5 daga cikin su, da su ka haɗa da shugaba mai ci yanzu, Joseph kabila, sun ajje takara independa, wato ba ƙarƙashin wata jam´iyar siyasa ba.

Daga jerin wannan yan takara akwai, tsofin shugabanin ƙungiyoyin tawaye, da ministoci, da kuma 3 daga mataimakaman shugaban ƙasa, na yanzu.

Kazalika, hukumar zaɓen ta amince ,da takara Nzanga Mubutu, ɗaya daga yayan tsofan shugaban ƙasar Zaire, Mubutu Sese Seko.

Hukumar zaɓen ta gabatar da sunayen yan takaran ga kotun ƙoli, wadda itace matakin ƙarshe, na amincewa, kokuma watsi da takardun shiga takara.

Bayan an ɗaage ranar 18 ga watan yuni, a mako mai zuwa ne, hukumar zaɓe, za ta bayyana sabuwar ranar shirya zaɓubuka a Jamhuriya demokradiyar Kongo.