1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun hallaka jami'an tsaro shida a Nijar

Salissou Boukari
June 1, 2017

Wasu mutane dauke da manyan makammai sun kai hari tare da hallaka jami'an tsaro shida a garin Abala da ke arewacin Jamhuriyar Nijar iyaka da kasar Mali.

https://p.dw.com/p/2dzGA
Niger Regierung Wache vor Sitz der Junta
Dakarun sojojin Jamhuriyar NijarHoto: AP

Mutanen da ke dauke da makkamai sun kai harin ne da yammacin jiya a garin Abala na Filingue da ke a nisan km akalla 200 a arewacin Yamai babban birnin kasar, iyaka da kasar Mali. Daga cikin wadanda suka mutun akwai sojoji hudu na "Garde National", da kuma jandarmomi biyu a cewar majiyar, wadda ta ce maharan sun kai wannan hari ne da misalin karfe bakwai na yammacin jiya kuma sun taho ne cikin motoci 14 masu ratsa dajin Sahara dauke da manyan makamman yaki.

Da safiyar wannan Alhammis ce aka yi jana'izar sojojin wanda Ministan cikin gidan kasar ta Nijar Mohamed Bazoum da sauran magabata suka halarta. A makon da ya gabata ma an kashe wasu 'yan sanda biyu da farar huda daya, a wani hari da aka kai a wani ofishin 'yan sanda cikin jihar ta Tillabery, iyaka da Burkina Faso.