1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan ta´adda na shirin kai hari a Belgium

Ƙasar Belgium ta tsaurara matakan tsaro a babban birnin ƙasar, wato Brussels. Shirin na a matsayin rigakafin hasashen kawowa ƙasar hari ne na ta´addanci. An ɗauki wannan mataki ne jim kaɗan bayan jami´an tsaron ƙasar sun sanar da cafke wasu tsageru ne 14, a safiyar yau juma´a. Wata majiya ta ce mutanen na shirin kai hare-hare ne na ta´addanci a cikin ƙasar. Hakan a cewar majiyar nada nasaba ne da ƙoƙarin tserar da wani ɗan ƙungiyyar Al-Qaeda dake tsare a gidan yari.